Sep 08, 2018 06:45 UTC
  • Zaben Shekara Ta 2019: APC Ta Bawa Shekarau Kujerar Sanata Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC mai mulkin jihar a jiya Jumma'a

Jaridar Primium times ta Najeriya ta bayyana cewa shekarau ya yi haka ne bayan haduwarsa da shuwagabannin jam'iyyar ta kasa wato Mr Adam Oshiomhole da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a gidansa a birnin Kano.

Kafin haka dai kakakin tsohon gwamnan Ya'u Sule ya shaidawa wata kafar yada labarai kan cewa mai gidansa zai ajiye jam'iyyar PDP ya koma APC labarin ya kara da cewa jam'iyyar ta bawa shekaratu gujerar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya bara jam'iyyar yake kuma son shiga takarar neman kujerar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

Shekarau yana daga cikin wadanda suka kafa Jam'iyyar APC amma kuma ya barta a shekara ta 2015 wanda yasa shugaban kasa na lokacin ya bashi ministan ilmi.

 

Tags

Ra'ayi