Sep 09, 2018 11:51 UTC
  • Rundunar Sojin Nigeriya Ta Kaddamar Da Hare-Hare Kan Sansanonin Kungiyar Boko Haram

Rundunar sojin saman Nigeriya ta kaddamar da hare-hare kan sansanonin mayakan kungiyar Boko Haram da suke shiyar arewa maso gabashin kasar.

Rundunar sojin saman Nigeriya a ta bakin kakakinta Air Kwamanda Ibikunle Daramola a jiya Asabar ta sanar da cewa: Jiragen saman yakin sojin Nigeriya sun kai wasu jerin hare-hare kan sansanonin mayakan kungiyar Boko Haram da suke shiyar arewa maso gabashin kasar musamman sansaninsu da ke dajin Sambisa.

Sanarwar ta kara da cewa: Jiragen saman yakin rundunar sojin ta Nigeriya ta ragargaza rumbun tsimin makamai mallakin 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram da suke cikin dajin Sambisa da kuma yankin tafkin Chadi tare da halaka wasu adadi na mayakan kungiyar. 

Tags

Ra'ayi