Sep 10, 2018 05:50 UTC
  • Shugaban Sudan Umar Albashir Ya Rusa Majalisar Ministocin Kasar

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya rusa majalisar ministocin kasar, tare da ayyana wani sabon Firayi minista.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir a jiya Lahadi ya rusa majalisar ministocin kasar, wadda ta kunshi ministoci 31.

Albashir ya sauke Bakar Hassan Saleh daga matsayin Firayi minista, wanda kuma dama shi ne mataimaki na farko ga shugaban kasa, wanda zai ci gaba da rike mukaminsa na mataimakin shugaban kasa kawai.

Jam'iyyar National Congress ta Hassan Albashir ta yanke shawar cewa daga yanzu mutum daya ba zai rike mukamin mataimakin shuban kasa da Firayi minista  a lokaci guda ba, inda a halin yanzu aka nada Mu'ataz Musa Abdallah tsohon ministan albarkatun ruwa  a matsayin sabon Firayi ministan kasar ta Sudan.

Albashir ya rage ministocin gwamnati daga 31 zuwa 21, sakamakon matsalolin tattalin arziki da kasar take fama da su.

 

Ra'ayi