Sep 10, 2018 05:51 UTC
  • Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka Dangane Da Hukuncin Kisa A Kan Muslim Brothers A Masar

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta yi kakkausar suka dangane da hukuncin kisa da kotun kasar Masar ta yanke a kan wasu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi (Muslim Brotherhood).

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta Amnesty Int. ta fitar a jiya ta bayyana hukuncin kisa da kotun Masar ta yanke a kan mambobin kungiyar 'yan uwan uwa musulmi su 75 da cewa abin kunya ne, kuma abin yin Allawadai.

Kungiyar ta ce tana kira ga mahukuntan masar da su gaggauta yin watsi da wannan hukunci da aka yanke wa wadannan mutane saboda suna adawa ta siyasa.

Amnesty Int. ta bayyana irin matakan da gwamnatin masar take dauka a kan 'yan adawar siyasa a kasar da cewa, matakai ne na kama karya, wadanda sun yi hannun riga da salon mulki na dimukradiyya.

Tags

Ra'ayi