Sep 10, 2018 05:52 UTC
  • Gwamnatin Kenya Ta Tsananta Dokoki A Kan 'Yan Gudun Hijira Da Suka Shiga Kasar

An zargi gwamnatin kasar Kenya da tsaurara matakai a kan 'yan gudun hijira na kasashen ketare da suke a cikin kasarta.

Tashar RFI bangaren faransanci ta bayar da rahon cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi jami'an tsaron gwamnatin kasar Kenya da cin zarafin 'yan gudun hijira ta hanyar gallaza musu a cikin 'yan kwanakin nan.

Bayanin kungiyoyin kare hakkin bil adama ya ce, sakamakon kafa sabbin dokoki kan 'yan gudun hijira da gwanatin Kenya ta yi, hakan ya baiwa 'yan sandan kasar damar cin karensu babu babbaka  akan fararen hula da suke gudun hijira  akasar, musamman 'yan kasar Sudan ta kudu, inda yanzu haka akwai daruruwa daga cikinsu da jami'an tsaron suke tsare da su.

A karshen watan Agustan da ya gabata ne gwanatin Kenya ta fara yin aiki da dokar shiga kafar wando daya da ''yan gudun hijira da suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba, wanda hakan ya jawo takun saka tsakanin gwamnatin kasar da kuma gwanatin kasar Sudan ta kudu.

Tags

Ra'ayi