Sep 10, 2018 12:43 UTC
  • Somaliya: An Kai Harin Kunar Bakin Wake Akan Wani Ginin Gwamnati

'Yan sandan Somaliya sun sanar a yau Litinin cewa wata mota mai makare da bama-bamai tare da matukinta sun kai harin kunar bakin wake a wata cibiyar gwamnati a birnin Magadishu

"Yan Sandan na Somaliya sun sanar da cewa; An kai harin ne a yankin Hawan dake cikin babban birnin kasar, yayin da shaidun ganin ido su ka cewa ginin da aka kai wa harin ya baci.

Sai dai majiyar 'yan sandan ta ce in ban da maharin babu wanda ya rasa ransa ko jikkata.

Kafafen watsa labarun kasar ta Somaliya sun kuma ba da labarin cewa an ji karar harebe-harbe acikin birnin na Somaliya, kamar kuma yadda aka ga hayaki yana tashi a saman babban birnin kasar.

Kungiyar 'yan ta'adda ta al-shabab ta dauki nauyin kai harin.

Tun a 1991 ne kasar Somaliya ta rasa tsaro da zaman lafiya wanda har ya zuwa yanzu yake ci gaba.

A shekarar 2011 ne kungiyar al-shabab ta bayyana wacce ta kwace iko da yankunan kasar da dama kafin daga baya a fatattake ta daga cikinsu.

 

Tags

Ra'ayi