Sep 10, 2018 12:46 UTC
  • Masar Ta Yi Watsi Da Bayanin Majalisar Dinkin Duniya Akan Hukuncin Kasa

Gwamnatin Masar ta bakin ma'aikatar harkokin wajenta ta bayyana baynin da ya fito daga Majalisar Dinkin Duniyar da cewa ba abin da za a lamunta da shi ba ne.

Kamfanin dillancin labarun Pars ya amabto shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet tana yin kira  da kada a aiwatar da hukuncin kisa akan 'yan kungiyar ikhwanul muslimin.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta ce; Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya tana fitar da hukunce-hukuncen marasa alkibla da rashin kwarewa.

A ranar asabar ne dai wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa akan yan kungiyar ikhwanul Muslmin sun 75 a karkashin abin da aka fi sani a kasar da batun Masallacin Rabi'atul Adawiyyah.

An kuma yanke hukuncin zaman kurkuku na har abada akan shugaban kungiyar wato Muahmmad Badi'i da kuma wasu mutane 47.

Tun bayan kifar da gwamnatin Muhammadu Mursi a 2013 ne gwamnatin Masar ta shigar da kungiyar 'Yan'uwa musulmi a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda. 

Tags

Ra'ayi