Sep 10, 2018 18:55 UTC
  • Ma'aikatan Kamfanin Man Fetur Na Kasar Libya Biyu Ne Yan Bindiga Suka Kashe A Birnin Tripoli

Yan bindiga sun kashe ma'aikatan kamfanin man fetur na kasar Libya biyu a wani harin da suka kai kan babban cibiyar kamfanin a birnin Tripoli a yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa akalla mutane biyu ne wasu yan bindiga suka kashe daga cikin ma'aikata a headquatan kamfanin man fetur na kasar Libya a yau Litinin sannan wasu akalla 10 sun ji rauni. Banda haka jami'an tsaro sun kashe yan bindiga biyu daga cikin wadanda suka kai harin. 

Labrin ya kara da cewa an dawo da ikon gwamnati a ma'aikatar bayan harin bayan fafatawa na wani lokaci. Wannan dai shi ne karon farko kenan da ake kaiwa kamfanin man fetur na kasar tun bayan faduwar gwamnatin Kazzaafi a shekara ta 2011.

Kafin haka dai yan bidigan sukan yi garkuwa da wasu rijiyoyin mai don neman wasu bukatunsu a wajen gwamnatin kasar. 

 

Tags

Ra'ayi