Sep 11, 2018 04:47 UTC
  • Mutane 35 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wata Tankar Gas A Nijeriya

Rahotanni daga Nijeriya sun ce alal akalla mutane 35 sun mutu kana wasu daruruwa sun sami raunuka sakamakon fashewar da wata tankar daukar iskar ta yi a jihar Nasarawa da ke kasar.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA ta ce lamarin ya faru ne a wani gidan mai dake hanyar Lafia-Makurdi lokacin da wata tankar da ke dauke da iskar gas ta yi bindiga da kuma kama wuta nan take.

Gidan talabijin din kasar NTA ya nuna hotunan da ke nuni da wuta tana ci bugu da kari kan tashin bakin hayaki, sannan kuma jami'an agaji suna ta daukar wadanda suka sami raunuka don kai su asibiti ko kuma wani wajen da za a yi musu magani.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari, cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ya isar da sakon ta'aziyya da kuma juyayinsa ga gwamnati da kuma al'ummar jihar Nasarawan sakamakon wannan hatsarin da ya same su, yana mai ba da umurnin da a dauki matakan da suka dace wajen kula da wadanda suka sami raunuka.

 

Tags

Ra'ayi