Sep 11, 2018 04:47 UTC
  • Sojojin Habasha da Eritrea Sun Rusa Kan Iyakokin Da Ke Tsakanin Kasashen Biyu

A ci gaba da kokarin da ake yi na zaman lafiya da kuma saukaka shige da ficen al'umma, dakarun kasashen Habasha (Ethiopia) da Eritrea suna ci gaba da rusa kan iyakokin kasashen na su.

Rahotanni sun bayyana cewar rusa kan iyakoki da shingunan tsaro da sojojin kasashen biyu suka kafa wani shiri ne na bude kan iyakokin kasashen biyu da ake shirin yi a yau din nan Talata.

A yau Talata 11 ga watan Satumban 2018 ne dai ake fara bukukuwan sabuwar shekarar kasar Habashan don haka ake ganin wannan bude kan iyakan yana daga cikin shirye-shiryen da aka tsara da nufin girmama wannan rana da kuma ba da gama ga al'ummomin kasashen biyu su sami damar shige da fice a tsakaninsu ba tare da wata matsala ba.

Kasashen Habasha da Eritrea sun mayar da huldar diplomasiyya a tsakaninu ne a ranar 16 ga watan Yuni wanda shi ne na farko a cikin shekaru ashirin na alakar kasashen biyu mai cike da sabani. Kungiyar Tarayyar Afirka dai ta yi na'am da wannan ci gaba da aka samu na tabbatar da sulhu da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

 

Tags

Ra'ayi