Sep 11, 2018 19:07 UTC
  • MDD Ta Goyi Bayan Kotun ICC Bayan Barazanar Amurka

Bayan barazanar da kasar Amurka ta yi wa Alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, wato ICC, Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya nuna goyon bayansa ga kotun.

Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya habarta cewa bayan barazana da mai bawa shugaban  Amurka shawara kan sha'anin  tsaro yayi ga alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC inda ya ce Amurka za ta dora takunkumi kan Alkalan kotun matukar suka hukunta Sojojin kasar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, kakakin Babban Sakataren MDD Stéphane Dujarric ya sanar da cewa Mista Antonio Gutterres na kara jadadda goyon bayansa ga kotun kan irin gudumuwar da take bayarwa na tabbatar da tsari a Duniya.

Cikin wata Sanarwa da ya fitar  mai bai wa shugaban kasar  Amurka shawara kan sha’anin tsaro John Bolton, ya bayyana kotun da ke birnin Hague da cewa take-takenta na da hatsari kuma Amurka ba za ta amince da su ba.

Bolton ya ce wasu daga cikin matakan da suke shirin dauka matukar kotun ta yi gigin tuhumar wani ba’amurke sun hada da hana alkalanta shiga kasar, sannan kuma ta rike kadarorinsu kafin daga bisani a nemi bangaren shari’ar kasar Amurka bayar da izimin kwace dukiyoyin alkalan.

A cikin watan nuwambar shekarar bara ne babbar mai shigar da kara ta Kotun Fatou Bensouda, ta ce za ta bukaci alkalai su fara bincike kan zargin da ake yi wa Amurka na aikata laifufukan yaki a Afghanistan.

  

Tags

Ra'ayi