Sep 11, 2018 19:09 UTC
  • An Cabke Mataimakin Babban Hafsan Sojin Kasar Comoro Kan Zargin Yunkurin Juyin Milki

Gwamnatin kasar Comoro ta kame mataimakin babban hafsan Sojin kasar a wani bincike na yunkurin juyin milki a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto wani na kusa da Ibrahim Salim mataimakin Babban Hafsan Sojin kasar kasar Comoro da ya bukaci a sakaye sunansa na cewa a jiya Litinin, jami'an tsaron kasar sun yi awan gaba da Salim bisa zargin yunkurin yiwa shugaban kasa Gazali Usman juyin milki, da kuma kai harin ta'addanci.

A watan Augustan da ya gabata ne babban alkain kasar ta Comoro Muhamed Abdu ya sanar da kame mutane biyar a binciken da ake yi na yunkurin juyin milki a kasar cikin wadanda aka kama harda marubucin nan kuma dan uwan tsohon mataimakin shugaban kasa Saeed Ahmed Saeed Turki.

Har ila yau kotun ta kasar Comoro ta sanar da hukuncin kasa da kasa na kame Jafar Saeed Ahmad Hasan mataimakin tsohon shugaban kasar ta Comoro.

Tags

Ra'ayi