Sep 12, 2018 07:08 UTC
  • Jami'an Tsaron Somaliya Sun Kame Wasu 'Yan Ta'addan Kungiyar Al-Shabab Ta Kasar

Rundunar tsaron Somaliya ta sanar da kame wasu 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ta kasar guda hudu a gefen birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

A wani samame da jami'an tsaron Somaliya suka kai yankunan da suke gefen birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a jiya Talata sun yi nasarar cafke wasu gungun 'yan ta'adda ta mutane hudu ciki har da wani babban kwamanda a kungiyar ta Al-Shabab.

Kakakin rundunar 'yan sanda a birnin na Mogadishu Qasim Ahmad Rubaleh ya bayyana cewa: Kafin kai ga nasarar kame 'yan ta'addan hudu, sai da aka yi dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya kai ga hasarar ran dan sanda guda tare da jikkata wani na daban.

Ahmad Rubaleh ya kara da cewa: Daya daga cikin kwamandojin kungiyar da aka cafke, tun a shekara ta 2015 jami'an tsaron kasar ta Somaliya suke farautarsa. 

Tags

Ra'ayi