Sep 12, 2018 11:53 UTC
  • Firaiministan Kasar Libya Ya Ce Har Yanzun Lokacin Gudanar Da Zabe A Kasar Bai Yi Ba

Firaiministan kasar Libya Fa'iz Suraj ya bayyana cewa rashin tabbataccen zaman lafiaya ya sa bai zai yu a gudanar da zabubbuka a kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Firaiministan yana fadar hakla ne a wata hari na musamman da ta hanasu a a yau Laraba, ya kuma kara da cewa matsalin tsaron kasar kamar yadda kowa ya shaida sun yi muni ta yadda ba zai yu a gudanar da zabubbuka kamar yadda kasar Faransa take bukata ba. 

A cikin watan Mayun da ya gabata ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya hada shuwagabannin kasar ta Libya inda suka cimma yerjejeniyar gudanar da zabubbuka a kasar a ranar 10 ga watan Decemba mai zuwa, tare da taimakon Majalisar dinkin  duniya. 

Suraj ya kammala da cewa ba zai yu a gudanar da zabe a yayinsa babu zaman lafiya a kan titunan kasar ba, kuma dole ne kowa ya amince da zaben kafin ya zama 'ingantacce.

 

Tags

Ra'ayi