Sep 17, 2018 19:06 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Hallaka Mutum 23 A Kasar Habasha

Jami'an 'yan sanda na kasar Habasha sun sanar da mutuwar mutum 23 sanadiyar rikicin kabilanci cikin wannan mako a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Alemayehu Ejigu shugaban 'yan sanda na yankin Oromia na cewa rikicin kabilanci ya salwanta rayukan mutum 23 a yankin -Burayu da kewaye sannan kuma ya raba sama da mutum 886 da mahalinsu.

Shugaban 'yan sandar ya ce ya zuwa yanzu an kame sama da mutum 70 da suke da alaka da wannan rikici.

Dangane da wannan rikicin,  Fitsum Arega shugaban Ofishin Piraministan kasar  Abiy Ahmed ya sanar a shafinsa na Twitter cewa Piraministan kasar ya yi tsananin kaduwa da jin wannan mumunan labari tare da yin allawadai da kisan mutanan da ba su ji ba su gani ba.

A nasu bangaren Al'ummar Adis Ababa fadar milkin kasar ta Habasha cikin fishi sun gudanar da zanga-zangar yin alawadai da wannan rikici a wannan Litinin.

Birnin Adis Ababa dai na dauke da mutane kuma kabilu daban daban kimanin miliyan hudu, amma kuma a yankin Oromia na birnin  kabilar Oromo ne suka fi yawa.

Tags

Ra'ayi