Sep 18, 2018 08:15 UTC
  • Sabuwar Gwamnatin Kasar Sudan Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki

Sabuwar gwamnatin kasar Sudan karkashin firaiminista Mutaz Musa Abdullahi ta yi rantsuwar kama aiki, a dai-dai lokacinda kasar take cikin tsananin matsalolin tattalin arziki.

Tashar talabijin ta Sky News Arabi ta bayyana cewa gwamnatin Firaiminista Abdullahi tana da ministoci 21 da kuma kananan ministoci 27, wato an rage yawan ministoci daga 31 zuwa 21 idan aka kwatanta da gwamnatin da ta shude.

Banda haka labarin ya kara da gwamnatin shugaban umar Hassan Al-bashir ta rage yawan jakadun kasar Sudan a kasashen waje don rage yawan kudaden da gwamnati take kashiwa harkar diblomasiyya a kasar.

Shugaban kasar yana fatan sabuwar gwamnatin kasar zata iya rage matsalolin tattalin arzikin da kasar take fama da su, musamman tashin farashin kayan bukatun yau da kullum wanda a cikin yan watannin da suka gabata ya kai kashi 65%. 

Tags

Ra'ayi