Sep 18, 2018 11:50 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Bukaci A Hada Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar Da Layin Dogo

Shugaban muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bukaci a hada dukkan tashoshin jiragen ruwan kasar da layukan dogo don sawwaka sauke kayayyaki zuwa cikin kasa.

Jaridar today ta Najeriya ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya litinin a wani jawabin da ya gabatar a taron kasa da kasa na tashoshin jiragen ruwa wanda hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta shirya a Abujha. 

Shugaban Muhammadu Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa tana kokarin tada komatsar tattalin arzikin kasar ne ta hanyar gina harsashen da ake bukata don yin haka. 

Shugaban  ya kara da cew a halin yanzu gwamnatinsa tana gina manya manyan tituna 25 da kuma hanyoyin 44 a shiyoyi 6 na kasar , sannan ya zuwa shekara ta 2021 ya na saran za'a samar da kekyawar tsarin sifira tsakanin kudanci da arewacin kasar.

 

Tags

Ra'ayi