Sep 18, 2018 14:59 UTC
  • Uganda Ta Zargi Tarayyar Turai Da Tsoma Baki Cikin Harkokinta Na Cikin Gida

Gwamnatin kasar Uganda ta zargi kungiyar tarayyar turai da tsoma baki a cikin harkokinta na cikin gida.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya gwamnatin kasar Uganda ta mayar da martani a kan rahoton da kudirin da majalisar kungiyar tarayyar turai ta fitar, wanda ke zargin gwamnatin Uganda da cin zarafin 'yan siyasa masu adawa.

A cikin bayanin da majalisar kungiyar tarayyar turai ta fitar ta bayyana cewa, jami'an gwamnatin Uganda sun kame 'yan majalisa biyu Robert Kyagulanyi, da kuma Francis Zaake, bisa hujjar cewa sun kai farmaki a kan tawagar motocin shugaba Yoweri Museveni, kuma an azabtar da su saboda hakan.

Gwamnatin Uganda ta yi kakkausar suka kan wannan rahoto na kungiyar tarayyar turai, tare da bayyana shi a matsayin shigar shugula a cikin harkokinta na cikin gida.

 

Tags

Ra'ayi