Sep 18, 2018 18:56 UTC
  • Libya: Sabon Fada Ya Sake Barkewa A Birnin Tripoli

Kamfanin dillancin labaru na Anatoli ya ce an rika samun fadace-fadace nan da can a cikin babban birnin kasar ta Libya tripoli

 A cikin sassa daban-daban na birnin Tripolin an rika jin harbe-harbe na manyan bindigogi daga cikin hadda kusa da filin saukar jiragen sama na kasa da kasa.

Bugu da kari an ga wata runduna ta mayakan da suke adawa da gwamnatin hadin kan kasa, a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin, suna fuskantar sojojin da suke biyayya ga gwamnati.

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar ta Libya Fayes al-Siraj ya yi gargadin cewa za su dauke tsauraran matakai akan dukkanin masu haddasa rashin zaman lafiya a cikin babban birnin.

Bangarorin da suke fada da juna sun sha karya tsagaita wutar yaki a tsakaninsu.

Tags

Ra'ayi