Oct 18, 2018 05:52 UTC
  • Najeriya : NLC Za Ta Gudanar da Zama Kan Batun Karin Albashi

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya, ta sanar da cewa a yau Alhamis mambobinta za su gudanar da wani zama domin tattauna batun karin albashin ma'aikata mafi karanci.

A wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran NAN a jiya Laraba, shugaban kungiyar kwadago ta NLC Ayyuba Wabba ya bayyana cewa, za su gudanar da zaman ne na yau Alhamis domin tattauna matakan da za su dauka kan batun karin albashi mafi karanci a Najeriya, wanda har yanzu suka kasa cimma daidaito a kansa tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

A 'yan kwanakin da suka gabata ne kungiyar ta shiga yajin yaki a fadin kasa kasa baki daya kan wannan batu, na neman a kara albashin ma'aikata da zai kai naira dubu 55 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikaci a Najeriya, bayan wata tattauanwa tsakaninsu da bangaren gwamnati, kungiyar ta janye yajin aikin, da zimmar cewa za a cimma daidaito.

Daga bisani gwamnati ta gabatar wa kungiyar da tayin Naira dubu 24 a matsayin albashi mafi karanci, amma kungiyar ta yi watsi da wannan tayi, inda a yanzu kowa ke jiran jin abin da kungiyar za ta fitar a zaman da mambobinta za su gudanar a yau Alhamis.

Tags

Ra'ayi