Nov 15, 2018 05:50 UTC
  • Najeriya : Kotu Ta Bada Umurnin Karbe Kudaden Bada Belin Nnamdi Kanu

Rahotanni daga Najeriya na cewa wata babbar kotun tarayya, ta bayar da umarnin da a karbe kudaden ajiya na bayar da belin jagoran 'yan aware na Biafra, Nnamdi Kanu.

Kotun ta ce za'a karbe kudaden ajiyar ne na wucin-gadi kudin da aka bayar da belin jagoran 'yan aware na kasar, Nnamdi Kanu da suka kai Naira Miliyan 300.

Hakan dai a cewar mai shari'a Binta Murtala Nyako, ya biyo bayan kasa gabatar da Nnamdi Kanu din a zaman kotun da aka yi. 

Mai shari'ar ta bayar da umarnin a ajiye kudin a asusun kotun, ba a asusun ajiya na gwamnatin tarayyar kasar ba, na TSA, kafin ranar da za a sake zaman shari'ar a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2019 mai zuwa.

Marabin da a ga Nnamdi Kanu, a Najeriya tun a watan Satumba na 2017, kafin sojoji su yi wa gidan iyayensa da ke Umuahia babban birnin jihar Abia, dirar mikiya.

Saidai jagoran 'yan awaren Biafra na kudu maso yammacin Najeriya Nnamdi Kanu ya bayyana a Isra'ila bayan da aka daina jin duriyarsa tun lokacin da sojoji suka kai samame gidansa.

A halin da ake ciki dai mai shari'ar kotun ta tarraya ta yi barazanar bayar da sammacin kamo mata wasu daga cikin wadanda suka tsaya wa jagoran 'yan awaren saboda rashin bayyanar su a zaman kotun da aka yi.

Tags

Ra'ayi