Nov 15, 2018 11:50 UTC
  • Gwamnoni A Najeriya Sun Bada Sharadi Na Amincewa Da Dubu 30 A Matsayin Mafi Karincin Albashi

Kungiyar gwamnoni a tarayyar Najeriya ta bayyana cewa zata biya albashi mafi karancin na naira dubu 30 ne kadai tare da wasu sharudda.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ne ya shaidawa yan jaridu haka a jiya Laraba bayan kammala taron gaggawa wanda gwamnonin suka kira a jiya Laraba a Abuja. 

Yari ya kara da cewa sun kafa kwamitin na gwamnoni 9 wadanda zasu gana da shugaban kasa don tattauna wannan batun. Har'ila yau ya ce sharuddan da suka shimfida sun hada da gwamnatin tarayyar ta sauya tsarin rabon kudaden kasa tsakaninta da jihohi, ko kuma kungiyar kwadago ta amince a rage yawan ma'aikata. 

Gwamnan jihar na Zamfara ya ce idan hakan bai faru ba ba wata jiha da zata iya bayin albashi na naira dubu 30 mafi karanci in banda jihar Lagos. 

 

Tags

Ra'ayi