Nov 16, 2018 06:35 UTC
  • Yammacin Afirka: Karancin Kudi Yana Yin Barazana Ga Aikin Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya

Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da cewa ayyukan tabbatar da zaman lafiya da dakarunta suke yi a yammacin Afirka yana fuskanatar barazana saboda karancin kudade

A wani rahoto na musamman da Majalisar Dinkin Duniyar ta shirya ta ambaci cewa; Masu ba da taimakon kudade na duniya, ba su bada ko da rabin kudin da su ka yi alkawalin bayarwa ba dangane da ayyukan zaman lafiya a yammacin Afirka

Da akwai rundunar tabbatar da zaman lafiya da ta fito daga kasashe biyar na yammacin Afirka da ke gudanar da aikinsu a cikin yankin.

A cikin shekarun bayan nan, kasashen da suke yammancin Afirka da kuma yankin Sahel suna fuskantar matsalolin tsaro da ayyukan ta'addanci musamman daga kungiyar boko haram

Ya zuwa yanzu dubban mutane ne su ka kwanta dama saboda rikice-rikicen da suke faruwa a cikin yankin da kuma hare-haren ta'addanci.

Tags

Ra'ayi