Nov 16, 2018 06:40 UTC
  • Gunea Conakry: Jami'an Tsaro Sun Tarwats Gangamin 'Yan Adawar Siyasa

Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake wajen tarwartsa masu Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a birnin conakry

"Yan adawar ne suna nuna kin yarda ne da keta yarjejeniyar da su ka cimma da gwamnati akan yin nade-nade na siyasa. Bugu da kari masu Zanga-zangar sun daga kwalaye da suke dauke da hotunan mutanen da jami'an su ka kashe a yayain ganagmin da aka yi a baya.

'Yan Sanda a kasar ta Gunea Conakry sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa duk wani gangami na nuna kin jinin gwamnati.

Daga lokacin da Alpha Conde ya zama shugaban kasa a 2010, daruruwa 'yan adawar siyasar ne jami'an tsaron su ka kashe.

'Yan adawar siyasar kasar na zargi shugaba Alpha Conde da yin mulkin kama-karya.

Ra'ayi