Nov 16, 2018 11:55 UTC
  • Mayakan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nigeriya Akalla Uku A Jihar Borno

Sojojin Nigeriya akalla uku ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar kan wani barikin soji a shiyar arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto daga wata majiyar sojin Nigeriya da ta bukaci a sakaye sunanta cewa: Gungun mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da farmaki kan barikin soji da ke garin Kareto mai nisan kilomita 150 daga birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin kasar a yammacin ranar Laraba da ta gabata, inda suka kashe sojojin gwamnatin kasar uku, kuma wasu sojoji da dama sun bata babu labarinsu.

Majiyar ta kara da cewa: Mayakan kungiyar ta Boko Haram sun fatattaki sojojin da suke sansanin amma bayan da jirgin saman yakin sojin kasar ya kawo musu dauki sun samu nasarar sake kwace iko da sansanin.

  

Tags

Ra'ayi