Nov 16, 2018 19:08 UTC
  • An Kashe Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Na MDD 8 D/Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an kashe dakarunta 8 a jamhoriyar Demokaradiyar Congo.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Majalisar Duniya na cewa kimanin Dakarun wanzar da zaman lafiya takwas ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 10 na daban suka jikkata yayin wani sumamen hadin gwiwa da dakarun tare sojojin kasar Congo suka kaiwa 'yan tawaye a garin Beni na jahar Kivo ta Arewa dake gabashin kasar.

Mambobin Kwamitin tsaron na MDD sun yi allah wadai da kisan dakarun wanzar da zaman lafiyar na Majalisar a kasar ta Congo.

farkon watan Disembar shekarar 2017 din da ta gabata ma an kashe dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin 15 a yankin na Beni.

Tags

Ra'ayi