Nov 18, 2018 19:10 UTC
  • Rikici Ya Kuno Kai Tsakanin Kungiyoyin ISIS Da Ash-shabab A Somaliya

Kungiyar ISIS a Somaliya ta ja kunan kungiyar Asha-shabab a game da duk wani zagon kasa da take yi mata yayin gudanar da ayyukanta

Kafar sadarwar (somal Al-jaded ta nakalto kungiyar ISIS din ta Somaliya na cewa lokaci ya yi da kungiyar za ta dauki fansa daga kungiyar Ash-shabab saboda irin zagon kasan da take yi mata  yayin gudanar da ayyukanta.

Wanan barazana na kungiyar ISIS na zuwa ne mako guda da mayakan kungiyar Ashabab din suka take wata tawaga daga kasar Masar da suka isa yankin Jubba na Somaliyan domin hadewa da kungiyar ta ISIS, inda suka kashe mutum guda tare da awan gaba da sauran mutanen.

Kungiyar ISIS din dake da sansaninta a manyan tsaunukan arewa maso gabashin Somaliya na kokarin samun gindin zama da wanzuwa a kasar to saidai hakan na fuskantar tirjiya daga Kungiyar Ashabab, inda kawo yanzu mayakan na Ashabab suka hallaka 'ya'yan kungiyar ta ISIS da dama.

Ra'ayi