Nov 20, 2018 09:24 UTC
  • Sojojin Kasar Aljeriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda Biyar

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da kashe 'yan ta'addar biyar a gabacin babban birnin kasar Alges

Sanawar ma'aikatar tsaron ta Aljeriya ta kunshi cewa: A karkashin yaki da ta'addanci da sojoji suke yi, sun yi nasarar halaka wani kasurgumin dan ta'adda a yankin Auladu Muhammad dake gundumar Milah mai nisan kilo mita 375 daga birnin Alges.

Wata majiyar ta kara da cewa sojojin sun kuma kashe wani 'yan ta'adda hudu a garin Kustantaniyyah da take a gundumar ta Milah.

Kasar Aljeriya ta dade tana fama da matsalar ta'addanci da 'yan ta'adda da suke son kafa gwamnati a kasar. A kan iyakar kasar da Tunisiya sojoji suna kokarin hana kutsen 'yan ta'adda

Tags

Ra'ayi