Nov 20, 2018 11:46 UTC
  • Matsalar Tsaro Na KaraKamari a Kan Yankunan Iyakokin Kasar Uganda

Kasar Uganda ta kara yawan dakarunta a yankunan dake iyakan kasar da jamhoriyar Demokaradiyar Congo sanadiyar tsanantar matsalar rashin tsaro.

Rahotani dake fitowa daga kasar ta Uganda sun ce cikin 'yan kwanakin nan an kashe masintar kasar 7 a tabkin Albert dake kan iyaka da kasar Congo,sannan kuma an hallaka 'yan tawayen Uganda biyu a yankin, lamarin da ya sanya 'yan tawayen suka fadada kai hare-harensu a yankunan kan iyakar kasar da jamhoriyar Demokaradiyar Congo.

Bayan hare-haren 'yan tawaye, kasar Uganda na fuskantar barazanar kwararar 'yan gudun hijra da wanzuwar cutar Ebola,da fashi da makami a yankunan kan iyakar kasar da jamhiriyar Demokaradiyar Congo.

A baya dai Gwamnatin ta Uganda ta sha sukar Majalisar Dinkin Duniya na kasa magance rikicin kasar Demokaradiyar Congo.

Ra'ayi