Nov 20, 2018 19:14 UTC
  • Adadin 'Yan Gudun Hijirar Sudan Ta Kudu Na Karuwa A Cikin Gida

Ofishin bayar da agaji na majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, adadin 'yan gudun hijira a cikin kasar Sudan ta kudu ya karu matuka.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, a bisa rahoton da babban ofishin bayar da agaji na majalisar dinkin duniya da ke birnin Juba na Sudan ta kudu ya bayar, adadin mutanen da suka yi gudun hijira a cikin kasar ya karu a cikin wannan wata.

Rahoton ya ce, a halin yanzu adadin mutanen da aka tsugunnar karkashin ofishin wannan hukuma, ya kai mutane dubu 970, wanda a cikin watan Oktoban da ya gabata adadin bai kai haka ba.

Wasu danganta karuwar adadin 'yan gudun hijirar ne da dawowar wasu da suka tsrere zuwa kasashe makwafta, musamman bayan dawowar tsohon madugun 'yan tawaye Dr. Reick Machar, wanda shi ne mataimakin shugaban kasa a halin yanzu.

Ra'ayi