Dec 08, 2018 18:22 UTC
  • Sojojin Masar Sun Halaka Wani Kwamandan 'Yan Ta'adda

Jaridar Yaum as-sabi ta kasar Masar ta dauki labarin da yake cewa sojojin kasar sun yi nasarar kashe Abu Malik al-Misri wanda babban kwamanda ne na 'yan ta'adda

A tsakiyar watan Nuwamba ma dai kungiyar 'yan ta'adda a kasar Masar ta fitar da wani faifai na Bidiyo da a ciki ta ke furuci da kashe kwamandojinta da sojojin Masar su ka yi daga cikinsu akwai Abu Usama Al- misry

Daga lokacin da Abdulfattah al-Sisy ya zama shugaban kasar Masar kungiyar Da'esh da wasu kungiyoyin na ta'addanci su ka tsananta kai hare-hare a cikin kasar ta Masar.

A yankin Sina a Arewa da akwai kungiyoyi na ta'addanci masu dauke da makamai da suke kai hare-hare a cikin sassa daban-daban na kasar Masar

Ya zuwa yanzu, yan ta'addar sun kasashe sojoji da 'yan sandan kasar Masar masu yawan gaske.

 

Tags

Ra'ayi