Dec 10, 2018 05:06 UTC
  • Morocco: Taron Kasashe Fiye Da 150 Kan Batun Hijirar Bakin Haure

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya kan batun gudun hijira ta sanar da cewa, sama da kasashen duniya 150 za su gudanar da taro yau a birnin Ribat na kasar Morocco, domin tattauna batun 'yan gudun hijira da kwararar bakin haure.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, babbar jami'ar majalisar dinkin duniya kan batun gudun hijira Louise Arbour, ta bayyana cewa kasashen da za su halrci taron za su tabbatar da yarjejeniya kan yadda za a yi ta'ammuli da 'yan gudun hijira a duniya ta hanyoyin da suka dace.

Ta kara da cewa fiye da kasashe 150 ne suka tabbatar da cewa za su halarci zaman tare da amincewa da abin da yarjejeniyar ta kunsa.

Sai dai a nasu bangaren wasu daga cikin kasashen turai sun nuna rashin gamsuwa da yarjejeniyar, musamman kasashen gabashin nahiyarv turai, inda suka ganin hakan zai kara bude kofa domin kwararar adadi mai yawa na 'yan gudun hijira a cikin kasashensu, yayin da ita ma Amurka ta nuna rashin gamsuwa da yarjejeniyar.

Louise Arbour ta ce ko da kasashen duniya za su taru a Morocco sun amince da yarjejeniyar, hakan ba zai mayar da ita kudiri da ya zama dole a yi aiki da shi ba, amma dai hakan zai taimaka matuka wajen magance matsalolida dama da ake fuskanta kan batun kwarar bakin haure a wasu kasashen duniya.

Ra'ayi