Dec 10, 2018 05:09 UTC
  • Somalia: Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Ta'addan Al-shabab Su 6

Jami'an tsaron kasar Somalia sun sanar da cewa, sun yi nasarar halaka mutum 6 daga cikin mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa ya bayar da rahoton cewa, a jiya Jami'an tsaron kasar Somalia sun sanar da cewa, a wani samame da suka kai kan maboyar 'yan ta'adda na Al-shabab a kusa da birnin Mogadishu, sun samu nasarar halaka mutum 6 daga cikin mayakan 'yan ta'addan.

Bayanin ya kara da cewa, 'yan ta'adda suna shirin kaddamar da wasu munanan hare-hare ne a cikin birnin na Mogadishu, inda bayan kashe 6 daga cikinsu, an kuma samu nasarar cafke mai jagorantarsu.

Mayakan kungiyar ta Al-shabab dai suna ci gaba da kara zafafa hare-harensu a cikin 'yan kwanakin nan a kan birnin Mogadishou, lamarin da ke salwantar da rayukan jama'a, da suka hada da jami'an tsaro da kuma fararen hula.

Ra'ayi