Dec 13, 2018 06:50 UTC
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Kasa Da Kasa Ta Soki Gwamnatin Najeriya Kan Kisan 'Yan Shi'a

Kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta ce har yanzu gwamnatin kasar ta Najeriya ta kasa daukar matakan da su ka dace akan kisan da aka yi wa 'yan shi'ar a 2015

Bayanin kungiyar kare hakkin bil'amar ta "Human Righr Watch' ya ce kisan na 'yan shi'a da jami'an tsaron kasar su ka yi, yana tattare da hatsarin jawo rashin yarda da tada kayar baya wanda zai kara dagula harkokin tsaro a kasar.

A watan Disamba na 2015 ne sojojin Najeriya su ka yi wa 'yan shi'ar kasar kisan kiyashi, tare kuma da kame shugaban 'yan shi'ar Sheikh Ibrahim Yakubu Al-zakzaky.

Tare da cewa kotun tarayya  ta yi kira da a saki shehun malamin, sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare shi tare da mai dankinsa Malama Zinat.

Ra'ayi