Dec 14, 2018 11:49 UTC
  • Bolton: Amurka Zata Yi Maganin Yadda Rasha Da China Suke Kutsawa A Kasashen Afrika

Mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan tsaron kasa John Bolton ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata kalubalanci kasashen Cana da Rasha a yadda suke fadada dangantakar tattalin arziki da sauri da kasashen Afrika

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Bolton yana fadar haka a jiya Alhamis a birnin Washington ya kuma kara da cewa babban burin Amurka a kasashen Afrika shi ne raya tattalin arzikin kasashen nahiyar da kuma tabbatar da diyaucin kasashen amma tare da samarwa kamfanonin kasashen Amurka wararen zuba jari da kuma kiyaye bukatun Amurka a kasashen.

Mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaron kasa ya ce a hakin yanzu kasashen biyu, wato Rasha da Cana suna ta fadada dangantakarsu ta tattalin arzikin da kasashen Afrika don toshe duk wata dama wacce Amurka zata samu na yin haka a kasashen Nahiyar. 

A cikin wannan shekara ta 2018 dai yakin tattalin arziki tsakanin kasashen China da Rasha a bangare guda da kuma Amurka a dayan bangaren sun rikita kasawannan duniya da dama.

 

Ra'ayi