Dec 15, 2018 06:31 UTC
  • An Kashe Mutane 11 A Rikicin Kasar Somalia

Majiyar jami'an tsaro a kasar Somaliya ta bada sanarwan cewa mutane akalla 11 suka rasa rayukansu a wani fafatawa da aka yi da magoya bayan tsohon dan kungiyar Al-shaba bayan da yansandan suka kama shi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya kara da cewa Mukhtar Robow wani jigo ne a cikin kungiyar yan ta'adda ta alshabab amma ya yi alkawarin barin kungoyar kuma ya barta, harma ya shiga takarar neman shugabancin daya daga cikin lardunan kasar.

Amma jami'an tsaro sun ce sun kama Mukhtar Robow ne saboda zarginsa da ya taimakawa wani yan ta'adda tare da makamansu zuwa wani yanki a kudu masu yammacin kasar.

Ma'aikatar cikin gida na kasar Somalia ya tabbatar da cewa an bukaci Mukhtar Robow ya yi watsi da ayyukan ta'adda ya kuma goyi bayan gwamnatin kasar a shekara ta 2017 wanda ya ce ya aikawa amma kuma an gano cewa har yanzun yana taimakawa yan ta'adda a kasar.

Ra'ayi