Dec 15, 2018 06:33 UTC
  • Sojojin Najeriya Sun Dage Haramcin Da Suka Yiwa Hukumar UNICEF

Sojojin Najeriya sun bada labarin dage haramcin da suka yi wa hukumar UNICEF mai kula da yara kanana ta Majalisar dinkin duniya, bayan da suka zargi wasu ma'aikatan hukumar da aikiwa yan ta'adda.

A jiya jumma'a ce sojojin Najeriya suka bada sanarwan haramtawa kungiyar da take khidiam ga yara ta MDD "UN children's agency Unicef" yin aiki a birnin Maidguri fadar jihar Borno a arewa maso gabacin kasar.

Sashen harshen ingilishi na BBC ya nakalto majiyar sojojin na cewa ta dage haramci na watanni ukku da ta yi wa hukumar a jiya jumma'a bayan tattaunawa da jami'an hukumar.

Labaran ya kara da cewa bayan tattaunawa da jami'an hukumar ta UNICEF sun bukacesu da su sanarda hukumomin da suka dace a duk lokacinda suke horar da sabbin ma'aikatansu".

Labarin dage haramcin ya zo ne jim kadan bayan da sojojin suka haramtawa hukumar aiki a jihar Bornon na tsawon watanni ukku, tare da zargin hukumar da tallafawa yan ta'adda.

Miliyoyin yaran yan gudun hijira a jihar ta Borno sun dogara da tallafin da suke samu daga kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa wadanda suka hada da hukumar ta UNICEF.

 

Tags

Ra'ayi