Dec 15, 2018 19:22 UTC
  • An Kai Harin Ta'addanci A Arewacin Kasar Kamaru

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambato cewa; Wasu mata biyu ne su ka kai harin kunar bakin wake a garin Kolofata da yake kan iyaka da Najeriya, wanda ya yi sanadin jikkatar mace guda da kuma wata budurwa yar shekaru 12

Majiyar jami'an tsaron kasar Kamaru ta ce maharan sun kutsa cikin kasar ta Kamaru ne daga tarayyar Najeriya da take kan iyaka.

Wannan dai shi ne karo na uku da aka kai harin kunar bakin wake a cikin mako guda a garin na Kolofata. Tuni aka tura da sojoji zuwa sassa daban-daban na birnin domin dakile hare-hare irin wadannan na kunar bakin wake.

A cikin shekaru 9 na bayan nan kungiyar Boko Haram ta addabi kasar Kamaru da sauran kasashen da suke a yankin tafkin Chadi ta kai hare-hare na ta'addanci

Kasashen Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru sun kafa runduar soja domin fada da kungiyar ta Boko Haram

Tags

Ra'ayi