Dec 16, 2018 06:54 UTC
  • Sojojin Habasha Za Su janye Daga Kan Iyakokin Eritrea

Rundunar sojin kasar Habasha ta sanar da cewa, dakarun kasar za su janye daga kan iyakokin kasar da kuma makwabciyarta Eritrea.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa,  a cikin wani bayani da rundunar sojin kasar Habasha ta fitar a jiya Asabar, ta sanar da cewa; dukkanin sojojin kasar da suke kan iyakokin kasar da Eritrea za su janye baki daya.

Bayanin ya ce a halin yanzu babu wata barazana da Habasha take fuskanta daga Eritrea, saboda haka babu wani dalili na jibge sojojia  an iyakokin kasashen biyu.

Kasashe Habasha da Eritrea dai sun kwashe tsawon shekaru 20 suna zaman doya da manja, sakamakon sabanin da suka samu kan batun iyakokin kasashen biyu, wanda ya jawo barkewar yaki na tsawon shekaru biyu a  tsakaninsu tun daga 1998 zuwa karshen 2000, a cikin watan Fabrairun 2001 kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a birnin Algiers na kasar Aljeriya, amma duk da dakatar da bude da suka yi, suna yi juna kallon hadarin kaji.

A cikin wannan shekara ne Firayi ministan kasar ta Habasha Abi Ahmad ya sake farfado da alaka tsakanin kasar da kuma Eritrea, inda suka sulhunta da juna.

 

 

Ra'ayi