Dec 16, 2018 06:55 UTC
  • An Sauke Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya sauke ministan harkokin wajen kasar.

Rahotanni daga birnin Bangui fadar mulkin jamhuriyar Afrika ta tsaklya na cewa, shugaban kasar Faustin-Archange Touadéra ya sanar da sauke Charles Armel Doubane daga kan mukaminsa na ministan harkokin wajen kasar, ya kuma maye gurbinsa da Sylvie Baipo-Temon, wanda zai ci gaba da rike mukamin ministan harkokin wajen Afrika ta tsakiya.

Shugaban na Afrika ta tsakiya bai yi wani bayani kan dalilan da suka jawo hakan ba, amma ofishinsa ya sanar da cewa, hakan yana daga cikin matakan da shugaban yake dauka ne na kyautata harkokin diflomasiyyar kasar.

Ko a ranar 1 ga wannan wata na Disamba da aka gudanar da tarukan cika shekaru 60 da kasar ta samu 'yancin kanta daga mulkin mallakar turawan Faransa, ba a ga ministan harkokin wajen kasar Charles Armel Doubane ba.

Ra'ayi