Dec 16, 2018 12:23 UTC
  • Gwamnatin Zambia Ta Karyata Zargin Cewa Kasar Sin Na Kokarin Kwace Iko Da Babbar Tashar Da Ke Samar Da Wutar Lantarki

Kakakin gwamnatin kasar Zambia Amos Chanda ya fada a jiya asabar cewa; Babu gaskiya a cikin Abin da John Bolton na Amurka ya riya na cewa; Kasar Sin na shirin kwace iko da tashar samar da wutar lantarki ta kasar a madadin bashin dala biliyan 10 da ta bayar

Chanda ya nuna takaicinsa akan yadda mai ba da shawara akan harkokin tsaro na Amurka ya bayyana, sannan ya kara da cewa; Ilahirin bashin da ke wuyan kasar bai wuce dala biliyan 9.7 ba, kuma dala biliyan uku ne kadai kasar Sin take bin kasar

Chanda ya kara da cewa; Da akwai takaici yadda babban jami'in gwamnatin Amurka yake da wannan bayanin da ba shi da tushe

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai mai bai wa shugaban kasar Amurka shawara akan harkokin tsaro John Bolton ya soki siyasar tattalin arziki ta kasashen Sin da Rasha a nahiyar Afirka, sannan ya ce Sin tana son kwace babbar tashar samar da wutar lantarki ta Zesco da ke kasar Zambia

Ra'ayi