Dec 16, 2018 14:51 UTC
  • DRC : An Dakile Hari Kan Wani Wurin Adana Kayayyakin Zabe

Hukumomi a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, sun sanar da cewa wasu yan bindiga sunyi yunkurin kai hari a wani wurin adana kayan hukumar zabe dake yankin Boni dake gabashin kasar.

Wannan dai na zuwa a yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da manyan zabukan kasar.

Wani Kakakin hukumar zaben ta CENi, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa sojoji da jami'an 'yan sanda sun murkushe yunkurin maharan na kai hari kan wurin adana kayan zaben, amma babu wani abunda ya faru da kayayayin da suka hada har da na'urorin zabe 2,000.

Wani bangare na jam'iyyun adawa a kasar dai na nuna rashin amincewa da gudanar da zabe ta hanyar na'urorin.

Idan ana tune a cikin daren Laraba data gabata ne wata mummunar gobara ta cinke kashi 80% na wata ma'ajiyar kayan zabe na Kinshasa babban birnin kasar.

A ranar 23 ga watan Disamba nan ne al'ummar kasar ta DR Congo zasu kada kuri'a a babban zaben kasar.

Tags

Ra'ayi