Dec 17, 2018 06:39 UTC
  • Nigeria: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hare-Hare  Kusa Da Maiduguri

Rahotanni daga Najeriya na cewa mayakan kungiyar Boko haram sun kaddamar da farmaki a kan kauyen Maiborti da ke tazarar kilo mita 5 daga wajen birnin Maiduguri na jahar Borno.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, mayakan na Boko Haram sun kaddamar da farmakin ne a yammacin jiya, kuma sun kona gidajen jama'a da dama, duk kuwa da cewa ba  samu rahoto kan rasa rayuka ba, amma dai ilahirin mutanen kauyen sun tsere, wasu shiga cikin Maiduguri, wasu kuma sun fantsama a cikin dazuka.

Wani mazaunin kauyen wanda kuma dan kato da gora ne mai suna Abacha Kaka, ya sheda wa kamfanin dilalncin labaran AFP cewa, daga bisani sojoji sun kai farmaki ta sama a kan mayakan na Boko Haram, wadnda kuma su ma daga bisani suka fice suka bar kauyen na ci da wuta.

Wannan hari dai na zuwa bayan makmancinsa da mayakan na Boko Haram suka kai a garin Gudumbali a cikin jahar ta Borno, inda a can ma suka yi barin wuta, kuma suka kashe wasu daga cikin sojojin Najeriya tare da kwasar tarin makamai da abinci, yayin da su ma sojojin na Najeriya suka ce sun kashe wasu daga cikin maharan.

Ra'ayi