Dec 24, 2018 19:03 UTC
  • Sojojin Kasar Sudan Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Shugaba Umar Hassan al-Bashir

A wani bayani da sojojin kasar ta Sudan su ka fitar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Umar Hassan al-Bashir domin kare cigaban kasa

Bayanin na sojojin Sudan ya ci gaba da cewa; Dukkanin jami'an tsaron kasar da su ka kunshi 'yan sanda da sojoji da jami'an leken asiri za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a karkashin doka.

Mataimakin shugaban kasar Sudan Faisal Hassan Ibrahim ya fada a jiya Lahadi cewa; Majalisar Tsaron kasar ta Sudan ta bai wa sojojin umarnin tsare da kare muhimman wurare a fadin kasar ta Sudan

Wannan matakin na sojojin ya zo a daidai lokacin da ake samun karuwar Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a cikin kasar.

Tags

Ra'ayi