Jan 10, 2019 19:28 UTC
  • An Tsayar Da Lokacin Da Za A Gudanar Da Manyan Zabuka A Kasar Libya

Manzon Musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Kasar Libya ne ya bayyana cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar

Cibiyar watsa labaru ta 'alwasat' ta ambato Gassan Salamah wanda shi ne manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libya yana bayyanawa a yau alhamis cewa;Majalisar Dinkin Duniya tare da dukkanin kungiyoyin kasar ta Libya sun yi tattaunawa akan gudanar da zaben 'yan Majalisa, sannan kuma gudanar da sauraron ra'ayin jama'a dangane da tsarin mulkin kasar gabanin karshen wannan shekarar ta 2019

Bugu da kari tattaunawar bangarorin biyu ta kunshi gudanar da zaben shugaban kasa

Gassan Salamah ya kara da cewa; Majalisar Dinkin Duniyar tana kuma tattaunawa da bangarori daban-daban na mutanen kasar da suka hada da 'yan siyasa da sojoji domin ayyana makomar kasar ta Libya

Har ila yau Gassan Salamah ya ce; Ya zuwa yanzu da akwai makamai har miliyan 15 a hannun mutanen kasar, sai dai hakan ba zai hana a ci gaba da tattaunawa ba

Libya ta fada cikin matsalar tsaro tun 2011 saboda tsoma bakin kasashen Amurka da turai, wnada ya kai ga kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi

Tags

Ra'ayi