Jan 16, 2019 07:05 UTC
  • Boko Haram Sun Kashe Mutane 10 A Najeriya

Kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta kai hari a yankin arewa maso gabacin Najeriya wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10

Kamfanin dillancin Reuters ya ambato majiyar tsaro daga kasar tana cewa; A jiya Talata ne 'yan kungiyar ta Boko Haram su ka kai hari a garin Rayon da ke Jahar Borno a yankin arewa maso gabacin Najeriya

A cikin kwanakin bayan nan kungiyar ta Boko Haram ta tsananta kai hare-haren ta'addanci a yankin arewa maso gabacin kasar, da ya hada da kashe sojojin kasar

Sai dai sojojin kasar ta Najeriya sun sami galaba a kan kungiyar tare da fatattakarsu daga garin Baga bayan kashe wani adadi mai yawa nasu

Tun a 2009 ne dai kungiyar ta Boko Haram ta fara kai hare-hare da makamai a yankin arewa maso gabacin kasar wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan fiye da mutane 20,000.

Fada da kungiyar Boko Haram, yana daga cikin manufofin da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya a gaba, sai dai ana samun koma baya a cikin fada da kungiyar ta 'yan ta'adda

Ra'ayi