Jan 16, 2019 10:06 UTC
  • Kenya : An Kawo Karshen Harin Al-Shebab A Nairobi_Uhuru

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyata, ya sanar da kawo karshen harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani Otel dake Nairobi babban birnin kasar, bayan shafe kusan sa'o'i 20 ana fafatawa da maharan.

Shugaba Uhuru wanda ke bayyana hakan a wani taron manema labarai, ya kuma ce an hallaka dukkan maharan. 

Alkalumman da mahukuntan kasar suka fitar sun nuna cewa mutum 14 ne suka rasa rayukansu a harin, kana wasu da dama suka raunana, a yayin da aka cewa sama da mutum 700 daga cikin ginin otel din. 

Saidai wata majiya daga asibiti ta ce gawawarkin mutum 15 aka kai a mutuwari, kuma gawawarkin sun hada dana 'yan Kenya 11, Ba'amurke guda da dan Biritaniya guda sai kuma wasu biyu da ba'a kai ga tantance gawawarkinsu ba.

Kungiyar Al'shebab ce dai ta dauki alhakin kai harin tun a jiya Talata.

Tags

Ra'ayi