Jan 16, 2019 10:27 UTC
  • ICC Za Ta Daukaka Kara Kan Sallamar Laurent Gbagbo

Masu shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC, zasu daukaka kara ga umurnin da wasu lauyoyin kotun suka bayar na sallamar tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, wanda ake zargi da cin zarafin bil adama.

A jiya ne dai alkalan kotun ta ICC ko kuma CPI, suka zartar da hukuncin sakin Mr Gbagbo, bisa cewar baida wani laifi, duba da yadda masu shigar da kara suka gaza bayar da gamsasshiyar shaida kan tuhume-tuhumen da ake masa, a don haka alkalan suka bada umarnin a sake shi ba tare da wata-wata ba.

Wani bayyani na kotun ta ICC da kamfanin dilancin labaren AFP ya samu, ya ce masu shigar da kara na kotun ta ICC, na shirin daukaka kara kan hukuncin alkalan, da ya bukaci a sallami M. Gbagbo, da tsohon na hannun damarsa Charle Ble Goude, ba tare da wata wata ba.

A cikin bayyani masu shigar da karar sun ce zasu iya amince da baiwa Laurent Gbagbo sakin talala a wata kasa, saboda ba zasu iya sallamarsa ba saboda wasu batutuwa dake alaka dashi.

M. Laurent Gbagbo, wanda shi ne wani tsohon shugaban kasa na farko da aka gurfanar a gaban kotun ta ICC, ana zarginsa da laifukan cin zarafin bin adama a tarzomar data biyo bayan zaben kasar a tsakanin 2010 zuwa 2011, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu uku a cikin watanni biyar.

Tsohon shugaban kasar ta Ivory Coast, ya kwashe shekaru bakai a hannun kotun ta ICC dake birnin Hague.

Tags

Ra'ayi