Jan 21, 2019 07:29 UTC
  • Obasanjo ya ce Buhari ya Shirya yin Magudi A Zaben 2019
    Obasanjo ya ce Buhari ya Shirya yin Magudi A Zaben 2019

Fadar shugaban kasa a Najeriya, ta mayar da martani kan kallaman tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo wanda ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da shirya magudi domin lashe babban zaben kasar dake tafe, tana mai danganta kalamman da abun mamaki da takaici, hasali ma a cewarta ''wauta ne''.

A sanarwar data fitar fadar shugaban kasar, ta ce zaben na watan Fabrairu za'a gudanar dashi cikin haske da adalci, kamar yadda shugaba Buhari ya yi alkawari wa 'yan kasar da duniya.

Cif Obasanjo, ya dai bayyana a cikin wata wasika, cewa shugaba Buhari yana aiki da jami'an tsaro da kuma manyan jami'an hukumar zabe domin ya samu nasara da gagarimin rinjaye a zaben da za'a gudanar a watan gobe.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da tsohon shugaban kasar ta Najeriya, Olusegun Obasanjo, ke sukan shugaba Buhari ba, wanda ya mara wa baya a waccen zaben na 2015.

Idan ana tune ko a watan Janairu 2018, Obansanji, ya bayyana a cikin wata budadiyar wasika cewa, bai kamata Buhari ya sake neman wani wa'addin mulki ba.

Ra'ayi