Jan 21, 2019 11:56 UTC
  • Najeriya: Gwamnatin Tarayyar Ta Bada Naira Billiyon 9.5 Don Tallafin Karatun Dalibai

Gwamnatin Najeriya ta bada Naira kimani Maira biliyon 9.5 don biyan kudaden karatu ga daliban kasar wadanda suke karatu a manya -manyan makarantu a ciki da kuma wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto ministan ilmi Malam Adamu Adamu yana fadar haka a wani taro a karshen makon da ya gabata.

Daraktan hukumar bada kudaden karatu na gwamnatin tarayyar Alhaja Asta Ndajiwo ce ta bayyana haka a madadin ministan Ilmi. Ta kuma kara da cewa, kafin haka  gwamnatin tarayyar kashe naira miliyon 800 don biyan dalibai yan Najeriya da suke karatu a ciki da wajen kasar a shekara ta 2018 da ta gabata.

Banda haka ministan ya bukuci hukumar bada kudaden karatu ta tsara aikinta don kawo karshen duk basussukan da dalibai suke bin ma'aikatar. 

Daga karshe ministan ya bukaci kungiyar malaman jami'o'i ASSU da kuma ta makarantun Kimiya da fasaha a kasar su kawo karshen yajin aikin da suke yi don tallafawa karatun dalibansu, da kuma faranta cikin iyayen daliban.

 

Tags

Ra'ayi